A ƙalla mutane bakwai suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa a ƙauyen Zhigiri na Ƙaramar Hukumar Shiroro ta Jahar Niger.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar daga cikin waɗanda suke mutu akwai Magidanci da ake kira da Mallam Mu’azu Babangida, matan sa guda biyu da Babban Ɗan sa.
Mai Magana da Yawun Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Shiroro Salis Mohammed Sabo, ya shaidawa majiyar mu cewa, lamarin ya faru a lokacin da Matafiyan ke kan hanyar su zuwa Dnaweto, maƙwabtan ƙauyukan domin halartar raɗin suna da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Lahadi.
“Kafin gina wannan madatsar ruwa ta Zungeru, tafiya zuwa waɗannan ƙauyukan a ƙasa ake yin ta domin babu ruwa. Don haka, kafin yanzu, wani baya buƙatar tafiya a saman ruwa, domin a ƙasa ake zuwa. Wannan na ɗaya daga cikin wahalhalu da madatsar ruwa ta Zungeru ta haddasa