Rochas Ya Baiwa Yan sanda Sa’o’i 24 Da Su Bayyana Laifin Sirikinsa

Sanatan Imo ta Yamma, Rochas Okorocha ya baiwa ‘yan sanda wa’adin sa’o’i 24 da su bayyana laifin surukin sa, Uche Nwosu a hukumance.

Okorocha ya sha alwashin daukar matakin shari’a don tilasta wa ‘yan sanda sakin Sirikin na sa, da ake zargin ‘yan siyasan ne ke rike dashi, idan har ta gaza biyan bukatarsa ​​nan da sa’o’i 24 masu zuwa.

An kama Nwosu wanda tsohon shugaban ma’aikatan Okorocha ne a ranar Lahadi a cocin St Peter’s Anglican Church, dake Eziama Obieri a karamar hukumar Nkwerre ta jihar.

Jami’an ‘yan sandan dauke da makamai sun kama Nwosu ne a lokacin da yake tsaka da ibada a coci, bayan an binne mahaifiyarsa.

Sai dai da yake magana da manema labarai a Owerri, babban birnin jihar, Okorocha ya ce: “Zan jira sa’o’i 24 don sanin abin da Nwosu ya yi. Muna son sanin laifinsa.

“Sa’o’i 24 sun isa ‘yan sanda su yi abin da ya dace. Ya kamata su sanar da duniya laifukan da ya aikata da kuma rashin yin hakan zan dauki matakin shari’a don neman a sake shi.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram