Bercelona Ta Sayi Ferran Torres Daga Manchester City

Dan wasan gaba na kasar Sipaniya Ferran Torres ya koma Barcelona daga Manchester City, inda ya rattaba hannu kan kwantiragi har zuwa watan Yunin 2027 kan Yuro biliyan 1 (£842m).

Dan wasan mai shekaru 21, ya koma Spain a kan fan miliyan 46.3 watanni 18 kacal bayan ya bar Valencia ya koma City.

Barcelona za ta biya £8.4m a matsayin kari kuma dole ne ta siyar da wasu ‘yan wasa don bin ka’idojin kudi na La Liga.

Kulob din ya samu damar daukar nauyin yarjejeniyar duk da matsalar kudi da yake fama da ita a halin yanzu sakamakon lamuni da ta samu a baya-bayan nan.

Torres dan kasar Spain ya buga wasanni 43 kuma ya ci wa City kwallaye 16 tun bayan komawarsa daga Valencia a watan Agustan 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram