Gwamnan jahar Katsina Aminu Bello Masari, ya sake jaddada kiransa ga al’umma musamman jama’ar jahar ta Katsina da su tashi tsaye wajen neman makaman da za su kare kawunansu a yayin da ƴan ta’adda suka kawo ma su hari.
Gwamnan ya ce bai yiwuwa a zo gabanka a wulaƙantaka a ci mutuncin ƴaƴanka da matanka kuma ka sa ido ka kyale.
Masari ya ce ai ba zata saɓu ba mutanen banza su ɗauki makamai amma a ce mutumin kirki ba zai riƙe makami ya kare kanshi ba.
Masari ya ce yana da kyau mutane su dage da maida bugu, ya ce a irin wannan in mutum ya rasa ranshi to yayi jihadi