Mutane 92 Suka Mutu A Najeriya Sanadiyar Cutar Zazzabin Lassa.

Adadin wadanda suka Mutu sanadiyar kamuwa da cutar zazzabin Lassa a Najeriya daga watan Janairun 2021 ya kai 92 yayin da jihohin Bauchi da Ebonyi suka samu karin mace-mace.

Cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta bayyana hakan a ranar Talata a rahotonta na baya-bayan nan game da barkewar cutar a kasar.

A cewar NCDC, mako na 50, wanda ya shafi ranar 13 zuwa 19 ga Disamba, ya bayyana cewa an sake samun karin mutuwar mutane uku a cikin makon da ake wannan nazari.

Yayin da Bauchi ta ba da rahoton wasu sabbin asarar rayuka biyu; Ebonyi ta sami sabon mutuwar mutum guda sanadiyar cutar.

“A dunƙule daga mako na 1 zuwa mako na 50, 2021, an sami rahoton mutuwar mutane 92 tare da karin (CFR) kashi 20.3 cikin ɗari, wanda ya yi ƙasa da Karin wadanda suka kamu da cutar a daidai wannan lokacin a cikin 2020 Wanda ke da (kashi 20.7),” in ji shi. .

NAN ta ruwaito cewa Najeriya na ci gaba da bayar da rahoton bullar cutar kuma ana kara gane cewa cutar ta bulla a yankuna da dama na yammacin Afirka kamar Jamhuriyar Benin da Ghana da Mali da kuma yankin kogin Mano (Sierra Leone, Laberiya da Guinea).

Hukumar ta kara da cewa an samu karin mutane 190 da suka kamu da cutar a jihohi 11 da kuma birnin tarayya Abuja, amma an tabbatar da bullar cutar guda 10 a jihohi hudu.

Sauran sun hada da: Edo – biyu, Ondo – hudu, Bauchi – uku, da Ebonyi – daya, kuma biyu daga cikinsu ma’aikatan lafiya ne.

Adadin sabbin wadanda da aka tabbatar, hukumar ta ce, daidai yake da adadin da aka bayar a makon da ya gabata.

“A cikin 2021, jihohi 17 sun sami akalla Mutum guda daya kamu da cutar, kuma aka tabbatar a cikin kananan hukumomi 66,” in ji shi.

“A cikin dukkan wadanda da aka tabbatar, Edo na da kashi 43, Ondo (kashi 35), da Taraba (kashi biyar).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram