Wani Kare A Ranar Kirsimeti Ya Yi Wuf Ya Cinye Ma Mai Maganin Gargajiya Ƴaƴan Maraina A Calabar

Wani mai maganin gargajiya mai suna Ani Ikoneto, ya rasa ransa bayan da karensa ya cire masa ƴaƴan maraina ya kuma cinye su a ranar Kirsimeti.

Jaridar Daiy Nigerian ta ce, jaridar Vanguard ta rawaito cewa, maƙwabtan Ikoneto, mai shekara 60 da yake zaune a layin Jebbs da ke Calabar ta kudu sun baiyana cewa ya je ya shawu ne a ranar Kirsimeti inda ya dawo gida a buge.

Wani maƙwabcin mai maganin, mai suna Itoro, ya ce “mu mun riga mun kwanta amma wasu kuma sun ci gaba da hira a waje. Da ya dawo sai ya shiga ɗakinsa ya kwanta kuma bai rufe kofa ba. Da yana baccin, sai ya yi kashi.

“Shi kuma karen sai ya ji warin kashin shi ya sa karen ya shiga ɗakin nasa domin ya ci kashin. To da ya hau kan gadon, sai ya damƙi ƴaƴan marainan shi, ko ya zaci nama ne,” in ji Itoro.

Ya ƙara da cewa ihu da mai maganin ya yi ne ya ja hankalin mutanen da su ke zaune su na hira, inda su ka kai masa ɗauki su ka ga abin da ya faru.

“Mu na jin ihun sa sai mu ka zaci ko ƴan daba ne su ka kai masa hari, muna shiga sai mu ka duk jikin sa jini kuma da alamun gaban sa ya fice, sai mu ka shima karen duk bakin sa jini.

Itoro ya ƙara da cewa kafin su kai Ikoneto asibiti sai da su ka wawwanke masa jikin sa saboda kashi da jinin da ya ɓata shi.

Ya ce a lokacin da su ke gyara jikin nasa yana ta zubar da jini sosai inda kafin ma su karasa asibitin rai ya yi halinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram