Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan fashin dajin ne, sun kai hari kauyen Gada da ke karamar hukumar Bungudu tare da kashe Hakimin yankin.
‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba
A daren ranar Talata ne suka mamaye yankin da manyan makamai tare da yi wa jama’a barazana
Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara ya tabbatar da faruwar lamarin
Ya ce gwamnatin jihar na aiki tukuru domin ganin ta kawar da irin wadannan miyagun ayyuka
Ibrahim Dosara a madadin gwamnati ya jajantawa al’ummar da abin ya shafa, da iyalan sarkin gargajiya da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su.
Al’ummomin da ke karkashin karamar hukumar Bungudu a ‘yan kwanakin nan sun fuskanci hare-haren ‘yan bindiga da ya kai ga kauracewar mazauna yankin da dama.