Ƴan sanda Sun Yi Ram Da Wani Matashi Mai Sace Ma Ƴan Mata Wayoyi Da Kuɗaɗe Bayan Ya Yi Lalata Da Su

Rundunar ƴan sandan jahar Katsina ta kama wani matashi mai
suna Usama Tijjani ɗan asalin jahar Kano mai shekaru 31 bisa laifin yaudarar ƴammata ya sace su kayayyaki da kuɗaɗe bayan ya gama lalata da su.

Kakakin rundunar ƴan sandan jahar SP Gambo Isah ne ya gabatar da matashin ga manema labarai a ranar Alhamis ɗinnan a farfajiyar hedikwatarsu da ke Katsina.

Usama dai yana yaudarar ƴammata ne ta hanya jawo ra’ayinsu a kafar sadarwar WhatsApp da Facebook yana ce ma su shi ɗan kasuwa ne mai ƙuɗi in suna son su samu ƙuɗi su zo ya kwana da su zai ba su naira subu 50.

Gambo Isah ya ce, dubun matashin ta cika a lakacin da ya yaudari wata yarinya ƴar asalin jahar Katsina inda ta yarda ta je ta same shi Kano ya sauke ta a wata Otel, bayan ya gama lalata da ita da safe da ta shiga wanka sai ya gudu da wayarta da sauran wasu kayayyaki na ta.

SP Gambo ya ce, bayan matashin ya gudu da wayar sai ya yi amfani da wayar ya ɗauki lambobin wasu ƙawayenta suma ya tura masu saƙo da nufin cewa ita ce tana shaida ma su ta samu wani mutum mai bada ƙuɗi in suna so suma su kirawo lambar za su samu ƙuɗi wurin mutumin kuma daga nan ya samu sa’arsu su suka je Zaria a jahar Kaduna suma ya yi amfani da su kuma daga baya ya gudu da wayoyinsu da wasu ƴan kuɗaɗe.

Da aka tambayi matashin ya amsa laifinsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram