An Kama Matashi Ɗan Shekara 20 Da Bindiga Yana Ƙoƙarin Satar Mutane A Zamfara

Rundunar Ƴan sandan Jahar Zamfara ta yi nasarar cafke wadi matashin ɗan ta’adda mai shekaru 20 mai suna Sani Mati wanda ake ma laƙabi da mai ƴanmata.

Kwamishinan ƴan sandan jahar, Ayuba El-Kana
ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Larabar da ta gabata.

El-Kana ya ce bayan kama ɗan ta’addar sun same shi da bindiga ƙirar AK-47 da harsasai a tare da shi.

Da aka ne mi jin ta bakin ɗan ta’addan matashin wanda ɗan asalin Ƙauyen Mayasa ne da ke ƙaramar hukumar Zurmi ta Jahar Zamfara,
ya amsa laifinsa haka zalika kuma ya ce bindigar ta mai gidanshi ce ya bashi yayi aikin ta’addancin da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram