EPL: Saka Na Tunanin Komawa Liverpool

Dan wasan gefe na kungiyar Arsenal da ke kasar Ingila, Bukayo Saka, ya nuna sha’awarsa ta komawa kungiyar Liverpool nan ba da jimawa ba.

Mai horas da kungiyar ta Liverpool, Jurgen Klopp, ya bayyana cewa, yana hankoron ganin Saka ya dawo buga wasa a kungiyar ne domin kara wa gaban kungiyar karfi yadda ya kamata.

Jaridar “Daily Post” ta ruwaito cewa, Saka da wakilansa na sha’awar canza shekar da za ta bai wa dan wasan damar buga gasar cin kofin kalubalen Turai, wato ‘Champions League’ da kuma lashe manyan kofuna.

Saka mai shekaru 20 da haihuwa ya samu kaiwa wani muhimmin matsayi ne a gasar Firimiya a cikin shekaru ukun da suka gabata inda ya buga wa kungiyar Arsenal wasanni 100, sannan ya buga wa kasar Ingila wasanni 14.

Ya ci wa Arsenal din kwallaye 6, ya kuma taimaka aka ci guda 4 a dukkanin gasanni a kakar wasanni ta bana.

Kwantaragin Saka da Arsenal dai zai kare ne a shekar 2024, kuma kungiyar za ta so ganin ta ci gaba da rike dan wasan nata mai hazaka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram