Najeriya Ta Samu Sabon Mai Horas Da Kwallon Kafa

Hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta sanar da nadin sabon mai horas da kungiyar Super Eagles mai suna, Jose Peseiro, wanda zai karbi ragama daga mai rikon kwarya, Augustine Eguavoen.

Sanarwar na kunshe ne a cikin wata takardar bayan taron kwamitin zartaswar hukumar ta NFF a ranar Laraba.

Nadin sabon mai horaswar ya zo ne bayan sallamar Gernot Rohr daga kungiyar Super Eagles.

Sai dai kuma hukumar ta bayyana cewa, mai rikon kwarya, Augustine Eguavoen, shi ne zai jagoranci kungiyar ta Super Eagles zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afirka, AFCON 2022, Wadda za a buga a kasar Kamaru, a yayin da dan kasar Portugal din, Peseiro, zai kasance a matsayin mai sa ido kawai.

Ana sa ran Peseiro ya kama aiki gadan-gadan a matsayin mai horaswar bayan kammala gasar ta AFCON ta 2022.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram