Rundunar Ƴan sandan Katsina Ta Kama Miyagun Makamai Tare Da Masu Laifi Su Kusan Dubu Ɗaya A 2021

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta ce, ta samu dimbin nasarori a wannan shekara mai karewa ta 2021 musamman a yakin da take da ayyukan ta’addanci da sauran manyan laifukka a fadin jihar.

Da yake jawabi ga ‘yan jaridu a hedikwatar rundunar a Katsina a kan nasarorin da aka samu a shekarar ta 2021, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sanusi Buba, ya ce, rundunar ta cafke jimlar mutane 999 da ake zargi da aikata laifukka daban daban a jihar.

Kwamishinan wanda mai magana da yawun rundunar, SP Gambo Isah ya wakilta, ya ce, rundunar ta samu wadannan nasarori ne duk da irin kalubalen da ta fuskanta, kuma hakan ya sanya an samu raguwar aikata laifukka a jihar idan aka kwatanta da shekarar 2020.

Buba, wanda ya samu karin girma daga mukamin kwamishina, CP, zuwa mataimakin Sufeto Janar, AIG, ya jinjina wa shugaban ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari da sarakunan Katsina da Daura bisa cikakken goyon baya da hadin kan da suka bai wa rundunar da ma sauran hukumomin tsaron da ke jihar.

Daga cikin mutane 999 da aka kama dangane da zargin aikata laifukka 608, a cewar kwamishinan, an gurfanar da 874 daga cikinsu a gaban kotuna daban daban domin fuskantar shari’a.

Haka nan kuma, an cafke wadanda ake zargi da fashi da makami 157, a yayin da aka kai 145 gaban kotu, sannan 12 na fuskantar bincike.

An kuma samu nasarar damke mutane 65 da ake zargi da garkuwa da jama’a, a yayin da aka aike da 63 kotu, 2 kuma
na fuskantar bincike.

Duk dai a cikin wannan shekara ta 2021, rundunar ta kama mutane 244 da ake zargi da satar shanu, aka gurfanar da 230 a gaban kotu, 14 na fuskantar bincike.

A yayin gudanar da ayyukakan ta na yaki da ta’addanci a jihar, rundunar ta hallaka ‘yan bindiga 38 a arangama daban daban da aka yi da su, a yayin da jami’an rundunar 5 suka kwanta dama.

Dabbobi kimanin 1,243 rundunar ta samu nasarar kwatowa daga bata-garin da suka hada da shanu 867 da tumaki 352 da awaki 24 da kuma Jaki guda 1.

An kuma ceto mutane 63 da aka yi safararsu, sannan aka kwato motocin sata 20 da kuma babura 18 daga barayi da ‘yan ta’adda.

Rundunar ta kuma kwace manyan bindigogi kirar GMPG guda 4 da kirar AK 47 guda 44 da kirar gida 20 da kuma hasasai kimanin 800 da dai sauransu.

Don haka CP Sanusi Buba ya kuma yaba wa ‘yan jaridu da hadin gwiwar hukumomin tsaro da al’ummar jihar da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon baya da hadin kan da suka bai wa rundunar a tsawon shekaru ukun da ya yi a matsayin kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram