Shaguna Kusan 200 Suka ƙone ƙurmus, Yayin da Gobara ta tashi a Kasuwanni biyu dake Sokoto

Gobara ta kone kasuwanni biyu, Kasuwan Daji da Kasuwar Kara da ke Sokoto a ranar Larabar da ta gabata tare da lalata kayayyakin da darajarsu ta kai na miliyoyin Naira.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gobarar da ta tashi da misalin karfe 11:30 na safe har zuwa yamma ta lalata sama da shaguna 150 a Kasuwan Daji.

Gobarar da ta tashi a kasuwar Kara da misalin karfe 7 na dare kuma tana ci har zuwa lokacin hada wannan rahoto tare da jami’an kashe gobara na tarayya da na jihar Sokoto suna fafatawa don kashe ta.

Kawo yanzu dai ba a iya gano musabbabin tashin gobarar guda biyu ba.

Kwamishinan kasuwanci da masana’antu, na jihar Bashir Jegawa, wanda ya ziyarci Kasuwan Daji, ya ce za a kafa kwamitin da zai tabbatar da barnar da aka yi domin bada tallafi ga wadanda su kayi asara.

Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta jihar Sakkwato, Alhaji Chika Sarkin Gishiri, ya ce ‘yan kasuwar sun yi asarar kayayyakin da suka kai na miliyoyin naira.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram