A karo Na Biyu, Hafsoshin Soji Sun Sha Alwashin Biyayya Ga Buhari Da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

Duk da irin caccaka da suke sha na tsawon shekaru da dama, Manyan Hafsoshin Sojin Najeriya, sun ƙara shan alwashin yin biyayya ga Shugaban Ƙasa na yanzu.

Sun sha wannan alwashin ne a ranar Alhamis, a lokacin saka naɗin girma da aka ƙarawa wasu manyan sojin Najeriya.

Ministan Tsaron Najeriya, Manjo-Janar Bashir Magashi ya buƙace su da su gudanar da ayyukan su cikin ƙwarewa.

Yayi jawabin ne a taron Soji daya wakana a Asokoro, Abuja a yayin da wasu Birgediya-Janar suka zamanto Manjo-Janar, inda Kanal da dama suka ɗare muƙamin Birgediya-Janar.

Magashi ya bayyana ƙarin girman a matsayin yin dubi akan irin jajircewar su, da sadaukarwa a aikin soji.

Ministan ya bayar da tabbacin cigaba da bayar da goyon baya ga Rundunar Sojin Ƙasa, na ƙarin wasu kayayyakin aiki a faɗin ƙasar.

Mai magana da yawun Rundunar sojin Ƙasa Birgediya-Janar Onyema Nwachukwu yace Babban Hafsan Sojin Ƙasa Laftanar-Janar Faruƙ Yahaya ya yi kira ga Janar ɗin da su zama masu biyayya ga Shugaban Ƙasa da Kundin Tsarin Mulkin Najeriya.

Yahaya ya tunatar dasu akan irin matsalolin tsaro, sai ya buƙace su dasu maida hankali domin samar da zaman lafiya da tsaro.

Acewar Nwachukwu a cikin wata sanarwa, Manjo-Janar Chijoke Owunle, a madadin Sojoji, ya sha alwashin yin biyayya ga Shugaban Ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram