Victor Osimhen da Dennis Emmanuel da Leon Balogun ba za su kasance daga cikin tawagar ‘yan wasan da za su buga wa kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ba a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2021.
An zare sunan Osimhen ne bayan da dan wasan ya harbu da cutar korona da kuma barazanar da kungiyarsa ta Napoli ta yi ta daukar matakin shari’a ganin cewa dan wasan bai jima da warkewa daga tiyatar da aka yi masa ba.
Shi kuma Dennis an ajiye shi ne bayan da kungiyarsa ta Watford ta bayyana cewa hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ba ta aike wa dan wasan da takardar gayyata a kan lokaci ba.
Raunuka ne suka yi sanadiyyar ficewar Leon Balogun da Abdullahi Shehu daga tawagar ta Super Eagles.
A sabili da haka ne aka dawo da Tyrone Ebuehi da Oluwasemilogo Ajayi cikin tawagar a yayin da Henry Onyekuru zai maye gurbin Osimhen, shi kuma dan wasan gaban da ke buga wasa a Jamhuriyar Czech, Peter Olayinka zai maye gurbin Dennis.
Kungiyar ta Super Eagles dai za ta buga wasan ta na farko ne a gasar ta AFCON da kasar Masar a ranar 11 ga watan Janairu, 2022, kafin daga bisani ta yi wasa da kasar Sudan da Guinea Bissau.