Da ɗumi-ɗuminsa: Buhari ya sanya hannu akan Kasafin Kuɗin Shekarar 2022 Na Naira Tiriliyan 17.126

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kudin shekarar 2022 na Naira Tiriliyan 17.126.

Shugaban ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar ne a ranar Juma’a a zauren majalisar Zartarwa da ke fadar shugaban kasa a Abuja, babban birnin tarayya (FCT).

Babban mai taimaka masa na musamman (Majalisar dattijai) kan harkokin majalisar dokoki ta kasa, Sanata Babajide Omoworare ne ya gabatar wa shugaban kasa kudirin kasafin kudin.

Yayin da shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin, shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ne suka mara masa baya.

Ministar Kudi, Kasafin Kudi, da Tsare-tsare ta Kasa, Mrs Zainab Ahmed, ita ma ta shaida rattaba hannu kan kasafin kudin na shekarar 2022 Mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram