Na Farko Shine Dambarwa Tsakanin Mahadi Shehu Da Gwamnatin Jihar Katsina:
Kamar yadda kowa ya sani, caccaka da sukar lamirin gwamnatin jihar Katsina da Mahadi Shehu ya ci gaba da yi gami da matakin da gwamnatin ta Masari ta dauka na maka shi kotu, ya matukar ja hankalin jama’ar ciki da wajen jihar Katsina a shekarar 2021.
Na Biyu Shine Gangancin Da Jami’an Kwastan Suka Yi:
A cikin shekarar ta 2021 ne kuma wasu jami’an hukumar kwastan ta Najeriya suka murje wasu mutane da mota har lahira a garin Jibia a sa’ilin da su ke kokarin cimma masu sumogar shinkafa kuma wannan lamari ya janyo cece-kuce daga jama’a, inda har ma gwamnatin jihar Katsina ta yi barazanar daukar matakin shari’a a kan hakan.
Na Uku Shine Aikin Gina Gadojin Kasa:
Kwangilar da gwamnatin Aminu Masari ta bayar ta gina manyan gadojin kasa a cikin birnin Katsina a kan kudi har nera biliyan 5.8 ya dauki hankali sosai ta hanyar ra’ayoyi mabanbanta domin kuwa a yayin da wasu mutane ke goyon bayan hakan, wasu kuwa cewa suka yi, ai ba abin da al’ummar jihar ke bukata kenan ba a halin yanzu.
Na Huɗu Shine Kisan Kwamishina:
Kisan gillar da aka yi wa Kwamishinan ma’aikatar kimiyya da fasaha ta jihar Katsina, Dr. Rabe Nasir, a cikin watan Disamban 2021 shi ma ya matukar daukar hankalin jama’a a wannan shekara mai karewa.