Ƙugiyar Ƙwadago Ta Yi Gargaɗi Game Da Matsalar Tsaro Tare Da Cewa Barazana Ce Ga Dimokraɗiyar Najeriya

Ƙungiyar ƴan Ƙwadago a Najeriya ta yi gargadin cewa halin da ake ciki na rashin tsaro a kasar barazana ce ga dimokradiyyar kasar.

Ta ce rashin tsaro da ya tabarbare ya wuce zama barazana ga harkokin rayuwa da tattalin arziki.

Ta kuma yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su himmatu wajen biyan bukatun al’umma domin samun ingantacciyar rayuwa a shekarar 2022.

Hakan na kunshe ne a cikin sakon sabuwar shekara daga shugaban kungiyar kwadago ta Kasa NLC, Ayuba Wabba.

Kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana karin farashin man fetur da gwamnati ke yi a duk shekara a matsayin canja sheka da gazawarta wajen sarrafa albarkatun kasa yadda ya kamata domin amfanin talakawa.

Ta yi alƙawarin yin amfani da kundinta na buƙatun da suka taso daga tarukan tsaro guda biyu wajen gabatar da buƙatu masu gamsarwa ga masu muradin shugabancin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram