Ma’aikatar kula da wutar lantaki ta tarayyar Najeriya ta bayyana shirin da take na samar da wutar lantarki mai karfin megawatt dubu 25 nan ba da jimawa ba.
A cewar sabon ministan ma’aikatar, Injiniya Abubakar Aliyu, ma’aikatar ta samar da na’urori da sauran kayayyakin aiki da dama a karkashin shirin shugaban kasa na bunkasa hasken wutar lantarki da nufin inganta lantarkin da ma sana’o’in da ke da alaka da lantarkin.
Aliyu ya bayyana hakan ne a Katsina a sa’ilin da ya kai ziyarar duba ayyukan tasoshin wutar lantarki a jihar ciki har da aikin samar da lantarki ta hanyar iska da ke Lambar Rimi a yankin karamar hukumar Charanchi.
Aikin na Lambar Rimi wanda aka bayar da kwangilarsa tun a watan Yunin 2009 na da nufin samar da megawatt 10 na wutar lantarki domin amfanin jihar kuma an sa ran kammala shi ne tun a wancan lokaci a cikin watanni 24.
Rahoton da muka samu ya nuna cewa dan kwangila na farko ya soma aikin ne a shekarar 2010 kuma bayan hakan sai aka sace injiniyan da ke kula da aikin a lokacin da aikin ya yi nisa, abin da ake ganin shi ne ya soma haddasa tsaikon kammaluwar aikin.