Babban Fasto, Da Wasu Mutane 5 Sun Mutu, A Wani Hadarin Jirgin Ruwa A Jihar Bayelsa


Wani Limamai mai shekaru 39 da matafiya biyar sun nutse a ruwa a lokacin da wasu kwale-kwale biyu suka yi karo da juna a kogin Ogbeinbiri da ke karamar hukumar Ijaw ta Kudancin jihar Bayelsa.

Har yanzu ba a ga wasu matafiya shida da ke cikin Kwale-Kwale ba, lokacin da hatsarin jirgin ruwan ya afku.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun ce daya daga cikin kwale-kwalen nada matsala, Kuma yana dauke ne da wata mata da ba ta da lafiya zuwa asibiti a garinYenagoa, babban birnin jihar a jajibirin sabuwar shekara inda ya yi karo da wani kwale-kwalen, inda ya kashe faston da wasu mutane biyar.

Faston da ya rasu an bayyana shi a matsayin babban mai kula da cocin Supernatural Church of God da ke unguwar Ogbeinbiri, yayin da wasu uku da hadarin ya rutsa da su ‘yan uwansa ne.

Matafiya sun yi tattaki ne da karfe 1:30 na safe duk da dokar hana zirga-zirgar dare a magudanan ruwa dake jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar Asabar jami’an ceto na cikin gida da ke neman wadanda suka tsira sun sami nasarar ceto mutum daya kacal.

Sun bayyana wadanda har yanzu ba a gansu ba kamar su Augustine Kieribo, Felix Azazi, Stephen Moses, mahaifiyar Adibo Kekere, matar Tou Kekere da Fasto Salvation Degema.

An dai bayyana cewa, ana zargin kwale-kwalen da ya yi jigilar mamacin ya yi karo ne da wani, yayin da zai kai wata mata mai matsakaicin shekaru zuwa Yenagoa domin duba lafiyar ta.

Tun da fari, Matar mara lafiyar, a cewar wata majiya ta al’umma yankin, an kwantar da ita a Asibitin Cottage da ke Ogbienbiri amma asibitin ba shi da iskar oxygen da ake bukata, Kuma hakan ya sa akayi yunkurin fitar da ita zuwa wani asibitin.

Sanata mai wakiltar Bayelsa ta tsakiya a majalisar wakilai ta kasa, Cleopas Moses, ya jajantawa al’ummar yankin Ogboinbiri da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu a hadarin jirgin ruwa.

Dan majalisar ya ce abu ne mai muni da jin labarin mutuwar irin wadannan mutane a yayin bikin sabuwar shekara.

Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, kamar yadda kakakinta, SP Asinim Butswat, ya yi alkawarin ganowa tare da mayar da martani ga manema labarai dangane da batu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram