Bikin Sabuwar Shekara: Ƴan Gida ɗaya Sun Nutse a Ruwa, Yayin Da Su Ka Je Iyo A Kogin Kwara

Wasu matasa biyu da aka ce iyayensu daya ne, Damilare Mai shekara (12) da Kamaldeen Mai shekara (14) a ranar Juma’a sun nutse a cikin kogin Asa a lokacin da suke yin iyo.

Jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Kwara ne suka tsinto gawarwakinsu daga kogin.

Lamarin wanda ya afku a kan titin Mubo na kogin, Maraba, Ilorin, ya jefa iyayen da mazauna garin cikin firgici da tausayi.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara Hassan Adekunle ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, “Mummunan lamarin ya faru ne da karfe 4:36 na yamma lokacin da wani mutum Mai suna Alhaji Eleja ya kira hukumar zuwa wurin da lamarin ya faru.

“Duk da haka, abin, abin takaici ne, ganin yadda ‘yan kwana-kwana suka tsamo gawarwakin mutanen biyu daga kogin.

“Wadanda suka mutu sun fito ne daga garin Ile-laru, yankin Sabo-Line, Ilorin wadanda suka je yin iyo tare da abokan su,” in ji shi.

Ya ce Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya bukaci al’uma musamman iyaye da malamai da su ci gaba da sanya ido kan yadda ‘ya’yansu ke tafiya, musamman a wannan lokaci na hutu, domin gujewa afkuwar irin haka nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram