Gwamnan Ondo Ya Yafe Ma Wasu Fursunoni Da Ke Tsare A Gidan Yari

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, ya yi afuwa ga wasu fursunoni 10 wadanda suke tsare a gidajen gyaran hali na Najeriya dake jihar.

An saki hudu daga cikin wadanda aka yi wa afuwa gaba daya yayin da sauran shidan da aka yanke musu hukuncin kisa a baya aka mayar da hukuncin nasu zuwa daurin rai da rai, An tattaro cewa matakin gwamnan shine bikin sabuwar shekara ta 2022.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a, Charles Titiloye, ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Gwamnan jihar Ondo, Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, SAN ya bada umarnin a gaggauta sakin fursunoni hudu (4) daga gidajen yari da ke jihar domin nuna murnar shiga sabuwar shekara ta 2022.

“Sakin fursunonin yana yin amfani da ikon da aka bai wa Gwamna ta hanyar sakin layi (a) (c) da (d) na sashe (1) na sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya, shekarar 1999 (kamar yadda aka yi wa gyara). An saki fursunonin ne bisa rahoton kyawawan halayen da suka nuna a cibiyoyin gidan gyaran halin.

“Gwamnan ya kuma mayar da hukuncin daurin rai-da-rai a kan wasu fursunoni shida (6) da aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya wadanda wasu kotuna a jihar suka yi. Gwamnan ya mika sakon taya murna da jin kai ga wani fursuna da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai. Yanzu zai shafe shekaru 15 a gidan gyaran hali.

“Gwamnan ya bukaci fursunonin da aka sako dasu dauki sakin nasu a matsayin wata dama ta rayuwa mai kyau a matsayinsu na ‘yan kasa dasu gyara. Ya kuma bukaci jama’a da su ba su masauki su mayar da su gida, kada a rika nuna musu wariya.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram