Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta yi kira ga ‘yan kasar da su yi amfani da sabuwar shekarar 2022 wajen farfado da soyayyar juna da hadin kai da kokarin tabbatar da kyakkyawan shugabanci a kasar.
Jam’iyyar, a cikin wata sanarwar ‘yan jaridu da mai magana da yawunta, Debo Ologunagba, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, samun ketare shekarar 2021 a karkashin mulkin jam’iyyar APC ya nuna irin bukatar da ke akwai ta kara kaimi da jajircewa wajen ceto kasar daga mummunan jagoranci.
Sanarwar ta kara da cewa, babu shakka, ikon Allah ne kawai ya ketarar da Najeriya a tsawon shekaru shiddan aka yi ana fama da matsalolin keta hakkin ‘yan Adam da da lalata al’amuran gwamnati da kashe-kashen jama’a da rashin ci gaba da talauci da karuwar ta’addanci da kuma satar kudaden gwamnati da ke faruwa a dalilin kama-karya da gazawar gwamnatin APC.
Don haka, a cewar sanarwar, sabuwar shekarar wata dama ce ta musamman ga ‘yan kasar ta su kau da duk wasu bambance-bambance da tsoro da gajeren tunani, sannan su fuskanci kalubalen da ke gabansu na tabbatar da kyakkyawan shugabancin da zai ceto Najeriya daga mummunan halin da ta shiga wanda ya yi daidai da manufofin jam’iyyar PDP.