Rundunar ƴan sandan jahar Zamfara ta shaida nasarar kuɓutar da wasu ƴara ƴan makaratar Islamiyya da suke kan hanyarsu ta zuwa har Katsina, daga harin ƴan fashin daji.
Kakakin rundunar SP Muhammed Shehu ne ya sanar da haka ga menama labarai a ranar Assabar ɗinnan a hedikwatar ƴan sandan jahar.
SP Shehu ya ce, ƴan ta’addan sun tare hanya ne daidai ƙauyen Kuche da ke yankin Gusau zuwa Funtua ta jahar Katsina a cikin daren jiya Juma’a inda suka ɗauke mutane daga cikin motoci biyar suka nufi daji da su.
Shehu ya ce tun lokacin da bin ya faru suka samu labari sai suka tura jami’ansu haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro inda suka samu nasarar kuɓutar da ƴaran ƴan Islamiyya su 21 waɗanda a cikinsu akwai mata biyu.
Ya ce an yi ba ta kashi tsakanin jami’an tsaron da ƴan ta’adda kafin daga bisani suka samu nasarar kwato ƴaran, ya kuma sanar da cewa malamin Islamiyyar da direban motarsu suna hannun ƴan ta’addan ba a samu damar kwato su ba tukuna.
Kamar yanda ya sanar ya ce ƴan Islamiyyar suna kan hanyarsu daga jahar Zamfara zuwa jahar Katsina domin halarta wani al’amari da a shafi harkar Islamiyya.
Hakazalika ya tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa don ganin an kuɓutar da malamin nasu da direban.
Daga ƙarshe kuma ya ja hankalin al’umma da su daina yin tafiyar dare saboda haɗarin da ke cikinta musamman a wannan lokaci na rashin tsaro.