Labari da ɗumi-ɗumi: Nafisa Abdullahi Ta Ce Ba Zata Ci Gaba Da fitowa Ba A Cikin Shirin “Labarina”

Fitacciyar jarumar fina-finan hausa, Nafisa Abdullahi wace ke fitowa a cikin shirin nan mai dogon zango mai suna “Labarina” ta sanar da daina fitowa a cikin shirin fim ɗin.

Nafisa wacce ta sanar da daina fitowar a saman shafinta na instagram, ta bayyana wasu dalilai da suka sanya ta yanke hukuncin barin fitowa a cikin shirin.

Daga cikin dalilan kamar yadda ta faɗa ta ce, tana da wasu hulɗoɗin kasuwancinta da kuma nata kamfanin da ta ke son ta fara yin nata fim ɗin a kwanan nan.

Jarumar ta ce bai kamata ba saboda ita fim ɗin ya tsaya.

Ta yaba ma kamfanin da ke shirya fim ɗin wato Saira Movies.

Daga ƙarshe kuma ta ba masoyanta hakuri bisa ga wannan hukunci da ta yanke.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram