Jami’an ‘yan sanda a jihar Legas sun kama wani magidanci mai suna Sola Kazeem mai shekaru 64 da haihuwa da kuma wasu mutane biyu bisa zargin mallakar kan mutum.
Rundunar ‘yan sandan ta yi ikirarin cewa mutanen uku da ake zargin suna gudanar da wata haramtacciyar aikine ta hanyar fakewa da hukumar tsaro mai suna Citizens for Peace and First Aid Mission of Nigeria, inda suka yanke kan wata gawa da aka binne a kusa da ofishin su da ke Ikorodu.
Kwamishinan yan sandan jihar Legas, Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (AIG), Hakeem Odumosu, yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin jiya a hedikwatar rundunar dake Ikeja, ya bayyana sunayen Wadanda ake zargi, da Israel Okon, mai shekaru 42; Joe Nwoke Charles, mai shekaru 35; da Ishola Kazeem mai shekaru 64.
Odumosu ya ce, jami’an hukumar sun gano wasu kwarangwal na mutane, harsashi guda 18, manyan bindigu na katako guda takwas, da laya, da motarsu ta Golf mai lamba USR 158 HP, a hannun wadanda ake zargi.
Ya ce an gano kokon kan dan Adam din ne daga hannun Kazeem, wanda ya furta cewa shi ma’aikacin kayan lambu ne.
AIG Odumosu ya ce, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala gudanar da bincike.