Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kaddamar da bincike kan mutuwar wani Dan basarake na Abuja, wanda ake zargin ya rasa ransa a otal, tare da wasu mutane hudu.
Marigayin Sa’adu Abubakar, jami’in hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), dan shugaban Pai ne da ke karkashin karamar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, amma yana zaune a Suleja ta jihar Neja tare da iyalansa.
An kama wani shugaban Unguwa a Suleja da wasu ‘yan mata uku da aka ce suna tare da shi a lokacin mutuwarsa.
Jaridar Daily Trust ta ce, a ranar Lahadin da ta gabata ta ruwaito cewa, an yi jana’izar marigayin ne a ranar Juma’a bayan da wasu dattawa suka shiga tsakani don ganin an amso gawarsa daga hannun ‘yan sanda.
Kokarin tattaunawa da jami’in ‘yan sandan dake kula da yankin (DPO) reshen ‘yan sandan Suleja, SP Mutala Mustapha, inda ake gudanar da shari’ar bai yi nasara ba.
Bai dauki ko mayar da kiran wayar da wakilin Majiyar mu ya yi masa ba.