Gwajin da Akayi Lionel Messi ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar Covid-19, kuma hakan yasa ya killace kansa, in ji kungiyarsa ta Paris Saint-Germain a yau Lahadi.
Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan PSG hudu da suka kamu da cutar gabanin wasan cin kofin Faransa da PGS din za ta Kara da Vannes.
Tauraron dan kasar Argentina na fama da rashin katabus a babban birnin na Faransa tun bayan ficewar sa daga kungiyar Barcelona a bazarar da ta gabata.
Messi ya zura kwallo daya kacal a wasanni 11 da ya buga wa PSG, sai dai Kuma ya zura kwallaye biyar a gasar zakarun Turai.
Ba zai samu damar buga wasan cin kofin na ranar Litinin ba, kuma da alama zai yi jinya a wasan farko na Ligue 1 na PSG tun lokacin hutun sabuwar Shekarar, da kungiyar za ta buga da Lyon ranar Lahadi mai zuwa.
Sauran ‘yan wasan da aka gwada sun hada da dan wasan baya Juan Bernat, mai tsaron gida Sergio Rico da matashin dan wasan tsakiya Nathan Bitumazala.
“A halin yanzu suna bin ka’idar Killace Kai, kuma suna bin ka’idojin kiwon lafiya da suka dace, musamman wurin dakile yaduwar cutar ta Corona,” in ji PSG.
Sai dai Kuma wannan lamari ya sanya Adadin mutanen da suka kamu da cutar ta Covid a Faransa ya haura 200,000 a wannan makon.pi