Dalibai 120 na Makarantar Sakandiren Bethel Baptist da aka Sace sun sami Ƴanci- Cewar CAN

Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya CAN reshen jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya tabbatar da cewa kawo yanzu an kubutar da dalibai 120 da aka sace na makarantar sakandaren Bethel Baptist da ke jihar Kaduna.

A wata sanarwa da ya fitar a Kaduna ranar Asabar, Hayab ya bayyana cewa da sanyin safiyar ranar 5 ga watan Yuli, 2021, ‘yan bindiga sun kai farmaki makarantar da ke Maraban Damishi a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna inda suka yi garkuwa da dalibai 121.

Ya ce adadin daliban da aka saki sun hada da dalibi daya da aka sako a ranar 28 ga watan Disamba, 2021 da kuma wani wanda aka saki a ranar 1 ga watan Janairu.

“Da sakin wadannan dalibai guda biyu, adadin dalibai 120 ne suka samu ‘yancinsu ya zuwa yanzu kuma dalibi daya ne ke hannun ‘yan fashin dajin,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram