Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum 6 A Jihar Ebonyi

A ranar Asabar din da ta gabata ne mutane shida suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da wata babbar mota da wata mota kirar Toyota Sienna a kan babbar hanyar Enugu zuwa Abakaliki.

Hatsarin ya afku ne a wasu ’yan mitoci kusa da garin Nkalagu na karamar hukumar Ishielu dake jihar Ebonyi.

Babbar Motar ta fito ne daga Abakiliki yayin da motar kirar Sienna mai kimanin fasinjoji bakwai ta nufi Abakiliki daga Enugu a lokacin da motocin biyu suka yi karo da juna.

Wakilin Jaridar Daily Trust da ke wurin da hatsarin ya afku, ya lura da cewa, wasu fasinjojin sun makale a cikin motar Sienan, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

Jami’an ‘yan sanda da masu goyon bayansu sun yi amfani da gatari wajen kokarin kubutar da wadanda hatsarin motocin suka rutsa da su domin kula da lafiyarsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram