Idan Ka Ce Kar Mutane Suyi Zanga-zanga Kamar Ka Ce Kar Su Fito Su Yi Zaɓe Ne – CNG Ga Masarai

Ƙungiyar mutanen Arewa, CNG ta bayyana damuwarta dangane da maganar da gwamnan jahar Katsina Aminu Masari yayi a bayabayan nan game da masu yin zanga-zanga saboda matsalar tsaro a faɗin jahar.

Kodinetan CNG, na shiyyar Arewa maso Yammacin Najeriya, Kwamret Jamilu Charanchi ne ya bayyana haka a wajen taron manema labarai da ƙungiyar ta kirawo a Katsina a ranar Lahadin nan.

Charanchi ya ce zanga-zanga dole ce saboda kundin tsarin mulki ya ba ƴan ƙasa dama su fito su yi zanga-zangar lumana madamar shugabancin da ake masu bai gamsar da su ba.

Kodinetan ya ce idan har Masari zai ce mutanen kar su yi zanga-zanga to kamar ya ce kar su fito su yi zaɓe ne.

Yana kuma mai shawartar gwamnan da ya hanzarta janye maganarsa da ya ce mutane su ɗauki makaman kare kansu.

Ya ce in gwamnan ya ce haka yana nuna gazawarshi ƙarara don haka ya ke ganin abinda ya kamata Masari ya yi shine ya ɓullo da hanyoyin magance talauci da rashin ilimi a tsakanin al’ummar.

A cewarsa waɗan nan sune ummul-haba’isin matsalar tsaro a faɗin jahar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram