An yi kira ga magoya bayan jam’iyyar PDP ta jahar Katsina da su daina ƙoƙarin haɗa mulkin tsohon gwamnan jahar, Ibrahim Shema da na gwamna Aminu Masari.
Tsohon janaral manaja na maaikatar gidaje ta jahar Katsina, Sirajo Aminu Maƙera ne ya bayyana haka .
Aminu Maƙera ya faɗi haka ne a wurin taron da jam’iyyar PDP ta jahar ta shirya a ranar Lahadin nan a babban ɗakin taro jam’iyyar da ke Katsina akan ƙudurinshi na tsayawa takarar Sanatan shiyyar Katsina a kakar zaɓe mai zuwa na 2023.
Maƙera ya ce abubuwan da Ibrahim Shema yayi a Katsina lokacin yana gwamna jam’iyyar APC sai ta shafe shekaru 40 ba ta yi kamarsu ba.
Don haka ya ce bai dace ba ma a rinƙa haɗa Shema da Masari a ɓangaren samar ma al’ummar Katsina romon ɗimokraɗiyya.