Wuta ta ƙone kimanin shaguna 250 a kasuwar Kayan abinci ta Obi Isiedo dake Okpuno-Egbu a Ƙaramar Hukumar Nnewi ta Jahar Anambra.
Jaridar Daily Trust ta tattara cewa shagunan gobara ce ta cinye su a daren 1 ga watan Janairun Sabuwar Shekarar 2022.
Wata majiya ta shaida cewa gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Asabar a wani shago guda ɗaya, inda ta fantsama zuwa wasu shagunan.
A cewar majiyar tankunan ruwa guda 7 aka sanya a wurin gobarar domin kashe ta, amma abun ya gagara.
Wani mazaunin kusa da kasuwar wanda gidan shi ya taɓu Chinedu Dike yace babu wanda zai iya bayyana abun da ya haddasa gobarar.
“Da kuke gani, gidana na kusa da kasuwa. Na dawo daga aiki, ina hutawa da misalin ƙarfe 9:30 sai muka ji tashi gobara, inda nan take mutane suka ruga a guje suna naiman taimako na tankokin ruwa, kuma an turo masu tankoki 7 amma basu magance gobarar ba.
Yace kimanin shaguna 250 zuwa 300 da kayayyakin su, suka ƙone ƙurmus.
Ya yi kira ga Gwamnatin Jahar Anambra, da Ƙungiyoyin bada tallafi, da mutane da su taimakawa waɗanda wannan iftila’in gobara ya shafa.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara na Jahar Anambra Martin Agbili Wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, yace ba’a rasa rai koda guda ɗaya.
Yace gobarar ta fara da misalin ƙarfe 10 na dare.