Ko Neman Aure Aka Je In Aka Bincika Aka Gano Mutum Ɗan PDP Ne To Yana Da Amana Don Haka A Bashi Ɗiya Ya Aura Kawai – PDP Katsina

Shugaban jam’iyyar PDP na jahar Katsina Salisu Yusuf Majigiri, ya ce duk wanda aka ce ɗan PDP ne to yana da amana sosai.

Majigiri ya bayyana haka ne a wurin wani taro da jam’iyyar ta shirya a hedikwatar ta da ke Katsina.

Ya ce yadda ƴan PDP suka iya mulki da riƙon amanar al’umma jam’iyyar APC ba ta iya shi haka ba.

Yana mai ce wa, ko neman aure aka je in iyayen yarinya suka bincika suka ji mutum lan PDP ne to su bashi aure kawai yana da amana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram