Rikicin Ribas: An Ga Mawaƙiya Teni Tana Sheka Gudu A Filin Jirgin Sama na Fatakwal

Mawakiyar, Teniola Apata, wacce aka fi sani da Teni, ta fitar da wani faifan bidiyo inda aka gan ta a guje a filin jirgin sama na Fatakwal a jihar Ribas.

Ta fitar da wannan bidiyon ne bayan wani wasan kwaikwayo da ta yi a garin Degema da ke karamar hukumar Asari Toru a jihar Ribas, ya samu cikas.

A cikin wani faifan bidiyo da ya mamaye intanet a ranar Litinin, an ga mawakiyar tana yin ma’anar daya daga cikin wakokinta mai suna ‘power Rangers’.

A cikin wannan Faifan Bidiyon dai an ji karar harbe-harbe, lamarin da ya kai ga mawakiyar da ’yan kallo sun yi ta tururuwa domin tsira da rayukansu.

A lokacin da tawallafa fai-fan bidiyan a shafinta na Instagram da aka tabbatar, Teni ta mayar da martani game da lamarin ta hanyar raba bidiyon da take gudu a filin jirgin sama.

A cikin rubutun da tayi, ta rubuta, “Da yanzu lamarin ya zamto wani labari na daban, amma ina godiya ga Allah. Ni kaina da dukan tawagarmu suna cikin koshin lafiya kuma mun dawo gida yanzu. Godiya ga masu kira da turo sakonnin Fatan Alheri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram