Wani Direba Ya Burmawa Matarshi Wuƙa Har Lahira A Jihar Adamawa

Ana Zargin Wani direba mai suna Muhammed Alpha dan shekara 57 a ranar sabuwar shekara ya burmawa matarsa ​​Hamsatu Wuka har lahira a garin Lande da ke karamar hukumar Gombi a jihar Adamawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a Yola ranar Lahadi.

Ya ce wanda ake zargin wani direban motar Kabu-Kabu ne dake unguwar Lande a karamar hukumar Gombi, ya daba wa matar sa, Hamsatu Muhammad mai shekaru 40 wuka, biyo bayan wata takaddama da ta barke a tsakaninsu.

Ya ce rigimar ta kai ga raba auren su da ya kwashe sama da shekaru 20.

Kakakin ‘yan sandan ya ce rundunar a ranar 1 ga watan Janairu, 2022, ta kama wani direban Kabu-Kabu mai shekaru 57 bisa laifin dabawa matarsa ​​‘yar shekara 40 wuka har lahira.

Ya ce bisa ga bayanan da aka samu daga hannun su, bayan rabuwar ta, matar ta koma wani gida kusa da gidan tsohon mijinta.

“A kokarinta na gyara sabon dakinta, ita (marigayi Hamsatu) ta cire wata kofa, na tsohon gidanta don gyara sabon gidanta.

“Ya fusata da matakin da ta dauka, wanda ake zargin ya yi amfani da wuka wurin daba wa matarsa ​​wacce ita ce mahaifiyar ‘ya’yansa takwas a wuya.

Nguroje ya kara da cewa, “Sakamakon raunin da ta samu, ta fadi kasa warwas, kuma aka garzaya da ita wani asibiti da ke kusa da yankin da lamarin ya afku, inda daga bisani aka tabbatar da mutuwarta.”

Ya ce rundunar ‘yan sandan garin Gombi ta kama wanda ake zargin ne biyo bayan rahoton da aka samu daga Malam Jauro Boka, wanda shi ne hakimin kauyen Lande.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Barde, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin, ya kuma shawarci jama’a da su guji daukar doka a hannunsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram