Ɓarin Wutar Sojoji: Turji Ya Cika Wandonshi Da Iska Ya Bar Mutane 68 Da Yayi Garkuwa Da Su Tsawon Watanni 3 Suna Hannunshi

Gawurtaccen ɗan bindigar nan Bello Turji ya sako mutane 68 maza da mata da yayi garkuwa da su kimanin watanni uku.

Kwamishinan Ƴansandan jahar Zamfara, Ayuba El-kana ne ya sanar da haka ga menema labarai a ranar Talatar nan.

El-kana ya ce wannan nasarar na zuwa ne saboda fatattakar ƴan ta’addan da rundunan sojin Najeriya tare da haɗin kan sauran jami’an tsaro a yankin dazukan da ƴan fashin dajin su ke ɓoye.

Shiga hoton ƙasa don kallon bidiyon

https://youtu.be/6F8C9rKk5Q8

Haka kuma Kwamishinan ya ce sun samu nasarar ceto wasu mutanen su 29 da suka haɗa maza da mata da mata masu ciki da masu goyon ƙananan ƴara, daga hannun ƴan bindiga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram