Idan Ba A Shawo Kan Matsalar Ƙarancin Ƙuɗi A Bankuna Ba Mutane Da Yawa Zasu Iya Mutuwa A Najeria – Afe Babalola

Sanannen masanin shari’ar nan na Najeriya, Afe Babalola, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalar karancin kudade da a halin yanzu bankunan kasar ke fama da ita.

Babalola, wanda kuma shine ya kirkiri jami’ar Afe Babalola da ke Ado-Ekiti, ABUAD, ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a Ado-Ekiti a ranar Litinin.

A cewarsa, matsalar idan ba a shawo kan ta a kan lokaci ba ka iya haddasa yunwa da talauci da mace-mace da karuwar aikata laifukka da rashin tsaro a fadin kasar.

A ‘yan kwanakin nan dai, babban bankin Najeria da bankunan kasuwanci sun saka masu hulda da su a kasar a cikin wani mummunan yanayi na karancin kudade.

Ya ce, ko a cikin jami’arsa, mutane ba su iya cire kudi ta na’urar ATM, sannan bankunan da ke makarantar ba su da kudaden da za su bai wa abokan huldarsu, sai dai an yi sa’ar dalibai na cikin hutu.

Babalola ya kara da cewa, bunkasar tattalin arzikin kasar ya fi dogara ne a kan cinikin ba ni- gishiri-in ba ka manda, inda ‘yan kasuwa kan yi musayar kayayyaki da kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram