Za A Ba Masu Auren Jinsi Damar Haihuwa A Israila

Ƙasar Isra’ila za ta bada dama ga masu yin auren jinsi ɗaya, yancin damar ɗaukar ciki ta hanyar bayar da hayar uwar da za ta ɗauki cikin.

BBC ta ruwaito cewa, wannan sanarwar, na zuwa ne bayan dokar da ke akwai ta cewa, ma’aurata namiji da mace da kuma matar da ke zaman kanta ne kawai ke da ƴancin ɗaukar cikin.

Wannan matakin dai zai kawo ƙarshen rashin adalci da nuna wariya na tsawon shekaru kamar yanda Ministan lafiya na Isra’ila, Nitzan Horowitz, ya ce.

Ƴan maɗigo da Luwaɗi a ƙasar sun daɗe suna neman ƴancin ɗaukar cikin ta hanyar saka maniyi a cikin wata kuma da za ta reni cikin ta haihu.

Bayar da damar zata fara aiki ne a ranar 11 ga Janairun wannan shekarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram