Bayan Shafe Shekaru 7 A Ofis, Buhari Ya Naɗa Mai Ba Shi Shawara A Kan Tattalin Arziƙi

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada wani farfesan tattalin arziki, Doyin Salami, a matsayin mai ba shi shawara a kan harkokin tattalin arziki.

Kafin wannan nadin dai, Salami shine shugaban hukumar mashawartan shugaban kasa a kan tattalin arziki.

Ayyukan babban mai bai wa shugaban kasar shawara sun hada da duba batutuwan da suka shafi tattalin arzikin cikin gida tare da gabatar da shawarwari a kan su ga shugaban kasa.

Jaridar “Premium Times” ta ruwaito cewa sanarwar nadin ta fito ne daga ofishin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin yada labarai, Femi Adesina.

Rahotanni sun nuna cewa, wannan shi ne karon na farko da shugaba Buhari ya nada mai ba shi shara ta fuskar tattalin arziki tun daga lokacin da ya karbi mulki a shekarar 2015.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram