Farashin Tumatur ya yi tashin Gwauron Zabi a Jihar Kano

Mazauna jihar Kano sun koka da yadda farashin Tumatur ke karuwa a kullum a jihar.

Wani mazaunin unguwar ‘Yankaba, Malam Umar Garba, ya ce tashin farashin tumatur yana da matukar tayar da hankali domin a nan ne ake noman sa, amma duk da haka farashin ya ci gaba da tashi.

A cewarsa, an sayar da kwandon tumatur mai kyau a kasuwar Yankaba kan kudi Naira 10,000 a makon da ya gabata sabanin N3,000 da aka sayar a watan Janairun bara. Ya ce masu sayan tumatur sun damu da tashin farashin, zai iya wuce abin da talaka zai iya siya nan ba da jimawa ba.

Wani bincike da jaridar Kano/Jigawa Chronicle ta gudanar ya nuna cewa a yanzu ana sayar da babban kwandon tumatur a tsakanin Naira 12,000 zuwa 14,000 wanda ba a saba gani ba musamman a irin wannan lokaci.

Sai dai bincike ya nuna cewa tsadar kayayyakin na iya kasance wa na da alaka da rufe babbar hanyar ruwa ta wuraren ban ruwa a kananan hukumomi biyar na jihar.

Rahotanni sun nuna cewa, an rufe madatsar ruwa ta Tiga a ranar 1 ga Nuwamba, 2021, wanda zai dauki tsawon watanni biyar, shi ne babban dalilin da ya jawo raguwar noman tumatur a jihar da kuma tsadar kayayyakin.

Wani manomin tumatur, Malam Yusuf Garun-Malam, ya bayyana cewa masu amfani da tumatur dole ne su yi hakuri domin da alama za a samu karancin tumatur ba kadai ba har ma da sauran ababe masu lalacewa a dawu, a jihar sakamakon rufe madatsar ruwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram