Fasinja Guda Ya Mutu Da Yawa Sun Jigata A Sokoto

Rahotanni sun bayyana cewa wani fasinja daya ya mutu yayin da wasu da dama suka samu raunuka yayin da wani da ake zargin dan fasa kwaurin ne ya kutsa kai cikin wata motar Kabu Kabu, yayin da yake kokarin tserewa daga Kamun Hukumar Kwastam

Lamarin wanda ya afku a kauyen Asara da ke kan titin Sokoto zuwa Illela, ya haifar da Rudani a yankin, sakamakon kona motoci guda biyu da suka hada da motar sintiri da motar jami’an Kwastam, da wasu mata gari suka yi.

Kakakin hukumar kwastam na yankin Sokoto, ASCI Tahir Yusuf, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce jami’an hukumar bisa sahihin bayanai sun kai farmaki kauyen Asara.

“Da misalin karfe 8 na safe ne aka tsayar da wata mota kirar Toyota Avensis dauke da gilashin kala-kala da ake kyautata zaton kayan fasa-kwauri ne, domin bincike amma direban ya yi kokarin tserewa, kuma ana cikin haka sai ga motar ta kuskure bige da daya daga cikin jami’an mu. Inda Kuma ta afkawa wata Motar Kabu kabu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fasinja guda yayin da wasu suka samu raunuka kuma an kai su wani asibiti da ke kusa da inda lamarin ya afku.

“Duk da haka, wasu marasa kishin kasa wadanda ba su da tausayi, suka Kai wa jami’an mu farmaki a wajen, kuma ana cikin haka ne suka banka ma motar sintiri daya da wata mota Mallakin daya daga cikin jami’an Mu wuta.

Ya ce an aike da karin jami’an tsaro yankin, domin tabbatar da doka da oda

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram