Aisha Buhari Ta Samar Ma Matasa Masu Buƙata Ta Musamman Da Ke Yi Ma Ƙasa Hidima Aiki

Uwargidan Shugaban Ƙasar Najeriya Aisha Buhari ta taimaka wajen samar wa, wasu tsaffin masu yiwa ƙasa hidima guda biyu Onogberie Efe Lulu da Nuruddeen Tahir aikin Gwamnati.

Wannan karamci na zuwa ne bayan buƙatar da Darkta-Janar na Hukumar Kula da Matasa masu yiwa ƙasa hidima Manjo Janar Shu’aibu Ibrahim yayi na taimakon masu ruwa da tsaki musamman a ɓangaren tallafawa matasa.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakin Darkta na ƴan jarida na Hukumar Emeka Mgbemena ya fitar, inda yace matasan guda biyu an miƙa masu takardar ɗaukar aiki daga Asusun ajiye kuɗi na Najeriya wanda Ibrahim ya miƙa masu a ofishin sa.

Ibrahim ya bayyana godiyar sa ga uwargidan shugaban Ƙasa data nuna goyon baya ga cigaban Hukumar NYSC da kuma cigaban Matasa.

Yace Wannan karamci zai ƙarfafawa waɗanda suka amfana su yi aiki tuƙuru ga ƙasa, Kuma su san cewa ana kulawa dasu.

Darkta-Janar ya taya waɗanda suka samu aikin murna ga aikin sa suka samu, sai ya buƙace su dasu zama masu aiki tuƙuru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram