Wasu magoya bayan mataimakin shagaban ƙasar Najeriya Farfesa Osinbajo sun fara girke wasu manyan hotunansa da ke nuna alamun yaƙin neman zaɓe a wasu ɓangarori na babban birnin tarayya, Abuja.
Baban sakataren ƙungiyar magoya bayan mataimakin shugaban ƙasar, Alhaji Musa Giɗaɗo ne ya shaida ma manema labarai dalilinsu na yin haka.
“Cancantarsa muka duba muka nemi ya fito takarar shugaban ƙasa a 2023, kuma muna ganin zai iya kawo mana abin da muke so a ƙasarmu”. In ji shi.