Babban Mai Taimakawa Shugaban Ƙasa akan Kafafen Yaɗa Labaru Garba Shehu ya bayyana cewar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ƴan Najeriya ne suka matsa mashi ya nemi Shugaban Ƙasa.
Yana maida martani ga wasu maganganu akan wasu shirye-shirye da Shugaban Ƙasa ya yi akan zaɓen Shugaban Ƙasa na Shekarar 2023.
A tattaunawa da Buhari ya yi, wanda gidan Talabijin na NTA ya watsa a ranar Alhamis, yace yayi bakin ƙoƙarin sa ga Najeriya, amma yana son ya zama bashi da ayyuka sosai bayan ya bar Shugaban Ƙasa a shekarar 2023.
Shugaban Ƙasar yace “akan shekaru na, ina ganin abokanai na, na hutawa, ina tabbatar maku da cewa, ina Son watanni 17 su zo, lokacin da zan zamanto bani da ayyuka sosai.
“Shekaruna na gaya mani, aiki daga karfe 6, 7 zuwa 8 a kullum a ofis, ba abun wasa bane. Na zama Gwamna, Minista, kuma ina wa’adin mulki na na biyu, don haka na daɗe a wannan tsarin, to mi zanyi ma ƙasa ta? Nayi bakin ƙoƙari na.
Dayake maida jawabi, Garba Shehu da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channel a shirin Sunrise Daily a ranar Juma’a, yace Shugaban Ƙasa nada damar da zaice yayi bakin ƙoƙarin sa ga ƙasar nan.