Ba Na Tunanin Ƴan Najeriya Za Su Ce Mani Allah Sambarka Bayan Na Bar Mulki

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce shi ba ya tsammanin ƴan ƙasar za su yaba mashi bayan ƴa bar mulki.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata fira da gidan talabijin na ƙasar, NTA, yayi da shi.

Buhari wanda ya ce ya bada iya gudunmuwar da zai ba ƙasar duba da shekara da shekaru da ya kwashe yana hidimta ma ƙasar ta hanyar riƙe madafun iko daban-daban.

“Me zan yi sama da abubuwan da na yi ma ƙasar nan?” ya ce.
Ya ci gaba da cewa yana fatan in ya ƙare wa’adin mulkinsa daga shekarar 2023, ƴan ƙasar za su gane cewa ya yi iya ƙoƙarinsa.

“Na yi gwamna na yi minista kuma gani a matsayin shugaban ƙasa a karo na biyu, don haka an dama da ni a harkar mulki, to me kuma zan yi sama da wannan?” Ya ce.

Na yi iya ƙoƙarina kuma ina fatan bayan na bar mulk, ƴan Najeriya za su yi duba na tsanaki. Ni ba na tsammanin wani yabo daga gare su, amma abinda na ke tsammani shine ƴan Najeriya za su ce mutumin nan ya yi iyakar ƙoƙarinsa. Wannan na ke tsammani daga ƴan Najeriya”. In ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram