Allah ya yi ma fitataccen malamin nan na Kano, Sheikh Ahmad Muhammad Ibrahim Bamba rasuwa.
Malamin wanda aka fi sani da Ƙala Haddasana ya rasu a yau juma’a bayan gajeruwar jinya.
Babban malamin ya yi fice a fagen karatuttukan Hadisi a masallacinsa mai suna Darul Hadis.
Za a yi jana’izar Dr. Ahmad bayan juma a masallacin na Darul Hadis da ke Kano.