Ma’aikatar kula da babban birnin tarayya, FCTA, ta bai wa wasu gidajen otal 4 da ke rukunin gidajen Mab Global a unguwar Gwarimpa a Abuja umarnin dakatar da ayyukan su ba da bata lokaci ba.
Shugaban hukumar kula birnin Abuja, AMMC, Umar Shu’aibu, ya bayar da umarnin a lokacin da ya kai ziyarar duba gidajen otal din a ranar Laraba.
Jaridar ‘Punch’ ta ruwaito tun da farko yadda aka canza wasu gine-gine 4 da ke rukunin gidajen zaman zuwa gidajen otal da dakunan shan barasa.
Da ma dai wasu mazaunan wurin sun rubuta wa hukumar raya babban birnin tarayyar, FCDA tun a ranar 5 ga watan Nuwamban 2021, suna kokawa a kan lamarin tare da rokon hukumar da ta tabbatar da bin doka ta hanyar mayar da gine-ginen zuwa matsayin su na asali na gidajen zama kadai.
Shu’aibu, wanda ya jagoran manyan jami’an hukumar ta MMC zuwa rukunin gidajen, ya fada wa masu otal-otal din cewa, ofishinsa ba zai lamunci matakan su na karya doka ba, sannan ya ba su wa’adin awoyi 48 na su tattara ya-nasu-ya-nasu su bar gidajen.