Tsohon Kociyan Real Madrid, Zidane, Zai Koma Aiki

Akwai yiwuwar tsohon mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke kasar Sifaniya, Zinadine Zidane ya koma horas da kungiyar PSG ta kasar Faransa.

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, Zidane zai karbi ragamar aikin ne daga mai horas da PSG din a halin yanzu, Mauricio Pochettino, a karshen kakar wasannin bana.

An sha alakanta Zidane din da komawa kungiyar PSG ko Manchester United ko kuma kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa domin ci gaba da aikinsa na horaswa.

Bayan zaman sa a kungiyar Real Madrid a karo na farko inda ya samu dimbin nasarori, Zidane ya ajiye aiki, sannan daga bisani ya sake komawa kungiyar a yayin da ta shiga halin kaka-nika-yi.

Sai dai Kociyan a karo na biyu bai samu damar lashe kofin zakarun turai ba, to amma ya jagorance su wajen cinye kofin La Liga karo na 34 a kakar wasanni ta 2019-2020.

Zidane ya ci gaba da zaman kashe wando tun daga lokacin da ya ajiye aikin na Los Blancos a karshen kakar 2020-2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram