Mutum 814 Sun Sake Kamuwa Da Covid-19 A Najeriya

Hukumar Kula da dakile Cututtuka masu yaduwa ta Najeriya, NCDC ta tabbatar da  cewa Akalla Mutane  814  ne suka sake kamuwa da cutar Covid-19 , wanda ya kawo adadin waɗanda aka tabbatar da sun kamu da cutar zuwa 247,009.

Hukumar NCDC ta bayyana hakan a shafinta na yanar gizo ranar Juma’a.

Adadin wadanda aka sallama a yanzu ya kai 217,832 da sai wadanda cutar tayi sanadiyar mutuwar su da suka kai 3066.

Hukumar NCDC ta lissafa Jihohin da aka samu bullar cutar a fadin kasar nan kamar haka;

‘Rivers-126, Taraba-76, Babban Birnin Tarayya Abuja-74, Ondo-68, Gombe-35, Kaduna-27, Oyo-20,Delta-17, Kwara-12, Ekiti-11, Bauchi-9, Edo-8, Kano -8, Nasarawa-7, Ogun-4 da kuma Bayelsa-2.’

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram